1 Sai mala’ikan da ya yi magana da ni ya komo ya farkar da ni, kamar yadda ake farkar da mutum daga barcinsa. 2 Ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?”
4 Na tambayi mala’ikan da ya yi magana da ni na ce, “Mene ne waɗannan, ranka yă daɗe?”
5 Sai ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?”
6 Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar
7 “Kai mene ne, ya babban dutse? A gaban Zerubbabel za a rushe ka ka zama fili. Sa’an nan Zerubbabel yă kawo dutsen da ya fi kyau, a kuma yi ta sowa ana cewa, ‘Allah yă yi masa albarka! Allah yă yi masa albarka!’ ”
8 Sai maganar
10 “Wa ya rena ranar ƙananan abubuwa? Mutane za su yi murna sa’ad da suka ga igiyar gwaji a hannun Zerubbabel.
11 Sai na tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan itatuwan zaitun guda biyu tsaye a hagu da kuma daman wurin ajiye fitilan fitilu?”
12 Na sāke tambaye shi na ce, “Mene ne waɗannan rassa biyun nan na zaitun a gefen bututu biyu na zinariya da suke zuba man zinariya?”
13 Ya amsa ya ce, “Ba ka san mene ne waɗannan ba?”
14 Sai ya ce, “Waɗannan su ne biyun da aka shafe don[a] su yi wa
-
a ko kuwa biyun da suke kawo mai su kuma