Ru’uya ta Yohanna
1 Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna, 2 wanda ya shaida dukan abin da ya gani, wato, maganar Allah da kuma shaidar Yesu Kiristi. 3 Mai albarka ne wanda yake karanta waɗannan kalmomin annabci, masu albarka ne kuma waɗanda suke jinsu, suke kuma sa abin da aka rubuta a ciki a zuciya, domin lokaci ya yi kusa.
4 Daga Yohanna,
8 “Ni ne Alfa da kuma Omega,” in ji Ubangiji Allah, “wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki.”
9 Ni, Yohanna, ɗan’uwanku da kuma abokin tarayyarku cikin wahala da mulki, da kuma haƙurin jimrewa da suke namu cikin Yesu, ina can tsibirin Fatmos saboda maganar Allah da kuma saboda shaidar Yesu. 10 A Ranar Ubangiji ina cikin Ruhu, sai na ji a bayana wata babbar murya kamar ƙaho, 11 wadda ta ce,
12 Sai na juya don in ga muryar da take magana da ni. Da na juya kuwa sai na ga alkukan fitilu bakwai na zinariya. 13 A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,”[a] saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa. 14 Kansa da kuma gashin fari ne fat kamar ulu, fari kamar dusar ƙanƙara, idanunsa kuwa kamar harshen wuta. 15 Sawunsa sun yi kamar tagullar da take haske cikin matoya, muryarsa kuma ta yi kamar muryar ruwaye masu gudu. 16 A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta.
17 Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce,
19
-
a Dubi Dan 7.13.