Zabura 99
 1 Ubangiji  yana mulki, 
bari al’ummai su yi rawan jiki; 
yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, 
bari duniya ta girgiza. 
 2 Ubangiji  mai girma yana a Sihiyona; 
an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai. 
 3 Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana, 
shi mai tsarki ne. 
 4 Sarki mai iko ne, yana ƙaunar adalci 
ka kafa gaskiya; 
a cikin Yaƙub ka yi 
abin da yake mai adalci da kuma daidai. 
 5 Ku ɗaukaka Ubangiji  Allahnmu 
ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa; 
shi mai tsarki ne. 
 6 Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, 
Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; 
sun kira ga Ubangiji  
ya kuwa amsa musu. 
 7 Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije; 
ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su. 
 8 Ya Ubangiji  Allahnmu, 
ka amsa musu; 
ka kasance wa Isra’ila Allah mai gafartawa, 
ko da yake ka hukunta ayyukansu marasa kyau. 
 9 Ku ɗaukaka Ubangiji  Allahnmu 
ku kuma yi sujada a dutsensa mai tsarki, 
 Languages
Languages