Zabura 95
 1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji ; 
bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu. 
 2 Bari mu zo gabansa da godiya 
mu rera gare shi da kiɗi da waƙa. 
 3 Gama Ubangiji  Allah mai girma ne, 
babban Sarki a bisa dukan alloli. 
 4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke, 
ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne. 
 5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, 
da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa. 
 6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, 
bari mu durƙusa a gaban Ubangiji  Mahaliccinmu; 
 7 gama shi ne Allahnmu 
mu mutanen makiyayansa ne, 
garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. 
Yau, in kuka ji muryarsa, 
 8 “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba,[~1~] 
kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa[~2~] a hamada, 
 9 inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, 
ko da yake sun ga abin da na yi. 
 10 Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; 
na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, 
kuma ba su san hanyoyina ba.’ 
 11 Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, 
‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”
<-  Zabura 94Zabura 96  ->
*Zabura 95:8 Meriba yana nufin faɗa.
†Zabura 95:8 Massa yana nufin gwaji.
 Languages
Languages