Zabura 92
Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci. 
 1 Yana da kyau a yabi Ubangiji  
a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka, 
 2 don a yi shelar ƙaunarka da safe 
amincinka kuma da dare, 
 3 da kiɗin molo mai tsirkiya goma 
da kuma ƙarar garaya. 
 4 Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji ; 
na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka. 
 5 Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji , 
tunaninka da zurfi suke ƙwarai! 
 6 Mutum marar azanci ba zai sani ba, 
wawa ba zai gane ba, 
 7 cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa 
kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, 
za a hallaka su har abada. 
 8 Amma kai, ya Ubangiji , za a ɗaukaka har abada. 
 9 Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji , 
tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; 
za a watsar da dukan masu aikata mugunta. 
 10 Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; 
an zubo mai masu kyau a kaina. 
 11 Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; 
kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana. 
 12 Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, 
za su yi girma kama al’ul na Lebanon; 
 13 da aka daddasa a gidan Ubangiji , 
za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu. 
 14 Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, 
za su kasance ɗanye kuma kore shar, 
 15 suna shela cewa, “Ubangiji  adali ne; 
 Languages
Languages