Zabura 84
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.[~1~] Na ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. 
 1 Ina misalin kyan wurin zamanka, 
Ya Ubangiji  Maɗaukaki! 
 2 Raina yana marmari, har yana suma, 
don filayen gidan Ubangiji ; 
zuciyata da namana na tā da murya 
domin Allah mai rai. 
 3 Har tsada ma ta sami gida, 
tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, 
inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta, 
wuri kusa da bagadenka, 
Ya Ubangiji  Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna. 
 4 Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; 
kullum suna ta yabonka. 
Sela
  5 Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, 
waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne. 
 6 Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, 
sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; 
ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna. 
 7 Suna ta ƙara ƙarfi, 
har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona. 
 8 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji  Allah Maɗaukaki; 
ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. 
Sela
  9 Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; 
ka duba da alheri a kan shafaffenka. 
 10 Rana guda a filayen gidan sun fi 
dubu a wani wuri dabam; 
zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna 
da in zauna a tentunan mugaye. 
 11 Gama Ubangiji  Allah rana ne da kuma garkuwa; 
ba ya hana kowane abu mai kyau 
wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai. 
 12 Ya Ubangiji  Maɗaukaki, 
mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.
<-  Zabura 83Zabura 85  ->
*^ Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.
 Languages
Languages