Zabura 65
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa. 
 1 Yabo ya dace[~1~] da kai, ya Allah, a Sihiyona; 
a gare ka za mu cika alkawuranmu 
 2 Ya kai wanda yake jin addu’a 
a gare ka dukan mutane za su zo. 
 3 Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu, 
ka gafarta[~2~] laifofinmu. 
 4 Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa 
ka kawo kusa don su zauna a filayenka! 
Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka, 
na haikalinka mai tsarki. 
 5 Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, 
Ya Allah Mai Cetonmu, 
begen dukan iyakar duniya 
da kuma na tekuna masu nesa, 
 6 wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, 
bayan ka kintsa kanka da ƙarfi, 
 7 wanda ya kwantar da rurin tekuna, 
rurin raƙumansu, 
da kuma tumbatsar al’ummai. 
 8 Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka; 
inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe 
kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki. 
 9 Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa; 
kana azurta ta a yalwace. 
Rafuffukan Allah sun cika da ruwa 
don su ba mutane hatsi, 
don haka ne ka ƙaddara.[~3~] 
 10 Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta; 
ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta. 
 11 Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka, 
amalankenka kuwa sun cika har suna zuba. 
 12 Makiyayan hamada sun cika har suna zuba; 
tuddai sun rufu da murna. 
 13 Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna 
kwari kuma sun cika da hatsi; 
suna sowa don farin ciki.
<-  Zabura 64Zabura 66  ->
*Zabura 65:1 Ko kuwa kan jira; ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba a tabbatar ba.
†Zabura 65:3 Ko kuwa ka yi kafara domin
‡Zabura 65:9 Ko kuwa don haka ne ka shirya ƙasar
 Languages
Languages