Zabura 149
 1 Yabi Ubangiji .[~1~] 
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji , 
yabonsa a cikin taron tsarkaka. 
 2 Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; 
bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu. 
 3 Bari su yabi sunansa tare da rawa 
suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya. 
 4 Gama Ubangiji  yana jin daɗin mutanensa; 
yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto. 
 5 Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma 
su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu. 
 6 Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu 
takobi mai kaifi kuma a hannuwansu, 
 7 don su ɗau fansa a kan al’ummai 
da kuma hukunci a kan mutane, 
 8 don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, 
manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe, 
 9 don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. 
Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. 
 Languages
Languages