Zabura 142
Maskil ne[~1~] ta Dawuda. Sa’ad da yake cikin kogo. Addu’a ce. 
 1 Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji ; 
na tā da muryata ga Ubangiji  neman jinƙai. 
 2 Na kawo gunagunina a gabansa; 
a gabansa na faɗa wahalata. 
 3 Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina, 
kai ne wanda ya san hanyata. 
A hanyar da nake tafiya 
mutane sun kafa mini tarko. 
 4 Duba ta damata ka gani; 
babu wanda ya kula da ni. 
Ba ni da mafaka; 
babu wanda ya kula da raina. 
 5 Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji ; 
Na ce, “Kai ne mafakata, 
rabona a ƙasar masu rai.” 
 6 Ka saurari kukata, 
gama ina cikin matsananciyar bukata; 
ka cece ni daga waɗanda suke fafarata, 
gama sun fi ni ƙarfi sosai. 
 7 Ka ’yantar da ni daga kurkuku, 
don in yabi sunanka. 
Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni 
 Languages
Languages