Zabura 126
Waƙar haurawa. 
 1 Sa’ad da Ubangiji  ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, 
mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki. 
 2 Bakunanmu sun cika da dariya, 
harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. 
Sai ana faɗi a cikin al’ummai, 
“Ubangiji  ya aikata manyan abubuwa dominsu.” 
 3 Ubangiji  ya aikata manyan abubuwa dominmu, 
mun kuwa cika da farin ciki. 
 4 Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji  
kamar rafuffuka a Negeb. 
 5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye 
za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki. 
 6 Shi da ya fita yana kuka, 
riƙe da iri don shuki, 
zai dawo da waƙoƙin farin ciki, 
 Languages
Languages