Zabura 125
Waƙar haurawa. 
 1 Waɗanda suke dogara ga Ubangiji  suna kama da Dutsen Sihiyona, 
wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada. 
 2 Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima, 
haka Ubangiji  ya kewaye mutanensa 
yanzu da har abada kuma. 
 3 Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance 
a kan ƙasar da take rabon adalai ba, 
domin kada masu adalci su yi amfani 
da hannuwansu su aikata mugunta. 
 4 Ka yi alheri, ya Ubangiji , ga waɗanda suke nagartattu, 
ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu. 
 5 Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi 
 Languages
Languages