Zabura 121
Waƙar haurawa. 
 1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, 
ta ina ne taimakona zai zo? 
 2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji , 
wanda ya kafa sama da ƙasa. 
 3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, 
shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba; 
 4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila 
ba ya gyangyaɗi ko barci. 
 5 Ubangiji  yana tsaronka, 
 6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba 
balle wata da dare. 
 7 Ubangiji  zai kiyaye ka daga dukan masifa, 
zai tsare ranka; 
 8 Ubangiji  zai kiyaye shigarka da fitarka 
 Languages
Languages