Zabura 113
 1 Yabi Ubangiji .[~1~] 
Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji , 
ku yabi sunan Ubangiji . 
 2 Bari a yabi sunan Ubangiji , 
yanzu da har abada kuma. 
 3 Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, 
a yabi sunan Ubangiji . 
 4 Ana ɗaukaka Ubangiji  a bisa dukan al’ummai, 
ɗaukakarsa a bisa sammai 
 5 Wane ne yake kamar Ubangiji  Allahnmu, 
Wannan mai zama a kursiyi can bisa, 
 6 wanda yake sunkuya yă dubi 
sammai da duniya? 
 7 Yakan tā da matalauta daga ƙura 
yakan ɗaga mabukata daga tarin toka; 
 8 ya zaunar da su tare da sarakuna, 
tare da sarakunan mutanensu. 
 9 Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta 
ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki. 
 Languages
Languages