Zabura 112
 1 Yabi Ubangiji .[~2~] 
Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji , 
wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa. 
 2 ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar; 
tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka. 
 3 Wadata da arziki suna a cikin gidansa, 
adalcinsa zai dawwama har abada. 
 4 Ko a cikin duhu haske kan haskaka wa mai aikata gaskiya, 
mai alheri mai tausayi da kuma mai adalci.‡ Ko kuwa / gama Ubangiji  mai alheri ne, mai tausayi da kuma mai adalci. 
 5 Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake, 
shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya. 
 6 Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba; 
za a tuna da mai adalci har abada. 
 7 Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba; 
zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji . 
 8 Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba; 
a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa. 
 9 Ya rarraba kyautansa ga matalauta, 
adalcinsa zai dawwama har abada; 
za a ɗaga ƙahonsa[~4~] sama da bangirma. 
 10 Mugun mutum zai gani yă kuma yi fushi, 
zai ciza haƙora yă kuma lalace; 
sha’awace-sha’awacen mugaye za su zo ga ƙarshe.
<-  Zabura 111Zabura 113  ->
*^ Wannan Zabura waƙa ce, layinta sun fara da jerin harufan Ibraniyanci bi da bi.
†Zabura 112:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya
‡Zabura 112:4 Ko kuwa / gama Ubangiji mai alheri ne, mai tausayi da kuma mai adalci.
§Zabura 112:9 Ƙaho a nan yana nufin girma.
 Languages
Languages