Zabura 111
 1 Yabi Ubangiji .[~2~] 
Zan ɗaukaka Ubangiji  da dukan zuciyata 
a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro. 
 2 Ayyukan Ubangiji  da girma suke; 
dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu. 
 3 Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, 
adalcinsa kuma zai dawwama har abada. 
 4 Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; 
 5 Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; 
yakan tuna da alkawarinsa har abada. 
 6 Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, 
yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai. 
 7 Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; 
dukan farillansa abin dogara ne. 
 8 Tsayayyu ne har abada abadin, 
ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya. 
 9 Yana ba da ceto ga mutanensa; 
ya kafa alkawarinsa har abada, 
tsarki da banrazana ne sunansa. 
 10 Tsoron Ubangiji  ne mafarin hikima; 
dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. 
Gare shi ne madawwamin yabo.
<-  Zabura 110Zabura 112  ->
*^ Wannan Zabura waƙa ce, layinta sun fara da jerin harufan Ibraniyanci bi da bi.
†Zabura 111:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya
 Languages
Languages