1 Mutanen Ruben da mutanen Gad, da suke da garken shanu da kuma garke tumaki masu yawa, suka ga cewa ƙasashen Yazer da Gileyad wurare ne masu kyau don kiwon shanu da tumaki. 2 Saboda haka suka zo wurin Musa da Eleyazar da kuma shugabannin jama’a, suka ce, 3 “Atarot, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo da Beyon, 4 ƙasar da
6 Musa ya ce wa mutanen Gad da mutanen Ruben, “Wato, sai ’yan’uwanku su yi ta yaƙi ku kuwa ku zauna nan? 7 Don me za ku karya zuciya Isra’ilawa daga hayewa zuwa ƙasar da
14 “Ga shi ku kuma, tarin masu zunubi, kuna tsaya a matsayin kakanninku, kuna sa
16 Sai suka zo wurin Musa, suka ce, “Muna so mu gina katangar dutse don dabbobinmu, da kuma birane don matanmu da ’ya’yanmu a nan. 17 Matanmu da ’ya’yanmu za su zauna a biranen da suke da katanga, don kāriya daga mazaunan ƙasar, amma mu, za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra’ilawa, har mu kai su wuraren zamansu. 18 Ba za mu koma gidajenmu ba sai kowane mutumin Isra’ila ya sami gādonsa. 19 Ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayin gabashin Urdun.”
20 Sai Musa ya ce musu, “In za ku yi haka, in za ku sha ɗamara da makamai a gaban
23 “Amma in ba ku yi haka ba, kun yi zunubi ke nan ga
25 Mutanen Gad da mutanen Ruben, suka ce wa Musa, “Mu bayinka za mu yi yadda ranka yă daɗe ya umarta. 26 ’Ya’yanmu da matanmu, garkunan shanunmu da na tumakinmu, za su kasance a nan biranen Gileyad. 27 Amma bayinka, kowane mutum a cikinmu zai haye a gaban
28 Sai Musa ya yi wa Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da shugabannin gidajen kakannin kabilan mutanen Isra’ila kashedi a kansu, 29 ya ce, “In kowane sojan mutanen Gad da na mutanen Ruben, ya ɗauki makaman yaƙi, ya haye Urdun tare da ku a gaban
31 Mutanen Gad da mutanen Ruben suka amsa, suka ce, “Barorinka za su yi abin da
33 Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.
34 Mutanen Gad suka gina Dibon, Atarot, Arower, 35 Atrot Shofan, Yazer, Yogbeha, 36 Bet-Nimra, da Bet-Haran a matsayin birane masu katanga, suka kuma gina katanga don dabbobinsu. 37 Mutanen Ruben suka sāke gina Heshbon, Eleyale, da Kiriyatayim, 38 haka kuma suka gina Nebo da Ba’al-Meyon (an canja waɗannan sunaye) suka kuma gina Sibma. Suka ba wa biranen da suka sāke ginawa sunaye. 39 Zuriyar Makir ɗan Manasse suka tafi Gileyad, suka ci ta da yaƙi, suka kori mutanen Amoriyawa da suke can.
40 Saboda haka Musa ya ba da Gileyad ga mutanen Makir, zuriyar Manasse, suka kuma zauna a can. 41 Yayir, wani ɗan Manasse, ya ci ƙauyukansu da yaƙi, ya kuma ba su sunan Hawwot Yayir. 42 Noba kuma ya ci Kenat da ƙauyukanta da yaƙi, ya kuma ba ta suna Noba, bisa ga sunansa.
<- Ƙidaya 31Ƙidaya 33 ->