1 “ ‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni. 2 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, ’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga
7 “ ‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba. 8 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da kuma ’yan raguna bakwai, ’yan bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani don daɗin ƙanshi ga
12 “ ‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga
17 “ ‘A rana ta biyu, a miƙa bijimai goma sha biyu, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 18 Tare da bijiman, ragunan da ’yan ragunan a miƙa hadayarsu da gari da hadaya ta sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade. 19 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya, don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadayunsu ta sha.
20 “ ‘A rana ta uku za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, raguna biyu, da kuma ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 21 Tare da bijiman, ragunan da ’yan raguna, a miƙa hadayun gari da hadayun sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade. 22 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
23 “ ‘A rana ta huɗu a miƙa bijimai goma, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 24 Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade. 25 A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
26 “ ‘A rana ta biyar a miƙa bijimai tara, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 27 Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan ragunan, a miƙa hadayu na gari, da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade. 28 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
29 “ ‘A rana ta shida a miƙa bijimai takwas, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 30 Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu ta gari da hadayu na sha bisa adadin da a ƙayyade. 31 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadaya ta sha.
32 “ ‘A rana ta bakwai a miƙa bijimai bakwai, raguna biyu da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani. 33 Tare da bijiman, ragunan da kuma ’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari, da hadayun sha bisa ga adadin da a ƙayyade. 34 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.
35 “ ‘A rana ta takwas kuwa za a yi tsattsarkan taro, ban da aikin da aka saba. 36 A miƙa hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga
39 “ ‘Ban da abin da kuka yi alkawari, da kuma sadakokinku na yardar rai, a miƙa waɗannan ga
40 Musa ya faɗa wa Isra’ilawa dukan abin da