1 To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe. 2 Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.”
3 Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.
4 Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka? 5 Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi[a] ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.”
6 Yesu ya ce,
10 Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su. 11 Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi.
12 A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
13 Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce,
16 Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.
17 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun. 18 Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce,
19 Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?”
20 Ya ce,
22 Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa,
23 Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.
24 Sai ya ce musu,
26 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
27 Yesu ya ce musu,
29 Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.”
30 Yesu ya ce,
31 Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.
32 Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa,
35 Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a. 36 Ya ce, “Ya Abba,[d]
37 Sai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus,
39 Ya sāke komawa, ya maimaita addu’ar da ya yi. 40 Da ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa.
41 Da ya koma sau na uku, sai ya ce musu,
43 Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron.
44 Mai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.” 45 Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba. 46 Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi. 47 Sai wani cikin waɗanda suke tsattsaye kusa ya zāre takobinsa, ya sare kunnen bawan babban firist.
48 Yesu ya ce,
51 Wani saurayin da ba ya sanye da kome sai rigar lilin, yana bin Yesu. Da suka yi ƙoƙarin kama shi, 52 sai ya gudu ya bar rigarsa, ya gudu tsirara.
53 Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru. 54 Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta.
55 Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba. 56 Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.
57 Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce, 58 “Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ” 59 Duk da haka ma, shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.
60 Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?” 61 Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba.
62 Yesu ya ce,
63 Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma? 64 Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?”
66 Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can. 67 Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau.
68 Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.[e]
69 Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.” 70 Sai ya sāke yin musu.
71 Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”
72 Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu.[f] Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa,
-
a Girik fiye da dinari ɗari uku
b Zak 13.7
c Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau biyu.
d Da Arameyik na Baba
e Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da ƙofar shiga zakara kuwa ya yi cara
f Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau na biyu.
g Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau biyu.