1 Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa, 2 ya ce musu,
4 Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan, 5 sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?” 6 Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su. 7 Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa. 8 Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki. 9 Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa,
11 Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.
12 Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa. 13 Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne. 14 Sai ya ce wa itacen,
15 Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru, 16 ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki. 17 Da yake koya musu, sai ya ce,
18 Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
19 Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka[e] bar garin.
20 Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa. 21 Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!”
22 Yesu ya amsa ya ce,
27 Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa. 28 Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?”
29 Yesu ya ce,
31 Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 32 In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.”
33 Saboda haka, suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.”
-
a Wani faɗi ne na Ibraniyanci mai ma’ana “Ceto!” Wanda ya zama kalmar yabo; haka ma a aya 10
b Zab 118.25; Zab 118.26
c Ish 56.7
d Irm 7.11
e Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da ya
f Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da zunubai. 26 Amma idan ba kwa yafewa, Ubanku ma da yake sama, ba zai yafe muku zunubanku ba.