1 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa, 2
3 Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas, 4 suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi. 5 Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su tā da rikici.”
6 Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, 7 wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.
8 Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa! 9 Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.”
10 Sane da wannan, Yesu ya ce musu,
14 Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci 15 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin. 16 Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.
17 A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
18 Ya amsa ya ce,
20 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun. 21 Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
22 Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya,
23 Yesu ya amsa ya ce,
25 Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?”
26 Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa,
27 Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa,
30 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
31 Sai Yesu ya ce musu,
33 Bitrus ya amsa ya ce, “Ko da duka sun ja da baya saboda kai, ba zan taɓa ja da baya ba.”
34 Yesu ya amsa ya ce,
35 Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.
36 Sa’an nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu,
39 Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce,
40 Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce,
42 Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce,
43 Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci. 44 Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi addu’a sau na uku, yana maimaita iri abu guda.
45 Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu,
47 Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su. 48 To, mai bashe shi ɗin, ya riga ya shirya alama da su, “Wanda na yi masa sumba, shi ne mutumin; ku kama shi.” 49 Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Sa’an nan ya yi masa sumba.
50 Yesu ya amsa ya ce,
52 Sai Yesu ya ce, masa,
55 A wannan lokaci sai Yesu ya ce wa taron,
57 Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru. 58 Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yă ga ƙarshen abin.
59 Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi. 60 Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito.
62 Sa’an nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?” 63 Amma Yesu ya yi shiru.
64 Sai Yesu ya amsa ya ce,
65 Sa’an nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon. 66 Me kuka gani?”
67 Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi 68 suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”
69 To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu mutumin Galili.”
70 Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.”
71 Sa’an nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”
72 Ya sāke mūsu har da rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”
73 Bayan ɗan lokaci, sai na tsattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.”
74 Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!”