1 Yoshuwa ya kira mutanen Ruben, mutanen Gad, da rabin kabilar Manasse 2 ya ce musu, “Kun yi duk abin da Musa bawan
6 Sai Yoshuwa ya sa musu albarka, ya sallame su, suka kuwa tafi gidajensu. 7 (Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manasse gādo a Bashan; sauran rabin kabilar kuma Yoshuwa ya ba su gādo tare ’yan’uwansu a yammacin hayin Urdun.) Sa’ad da Yoshuwa ya sallame su su tafi gida, ya sa musu albarka, 8 ya ce, “Ku koma gidajenku tare da dukiya mai yawa, babban garken dabbobi, azurfa da zinariya, tagulla da ƙarfe, da tufafi masu yawa sosai, sai ku raba ganimar da kuka samu daga abokan gābanku, da ’yan’uwanku.”
9 Saboda haka sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, suka bar Isra’ilawa a Shilo cikin Kan’ana don su koma Gileyad, ƙasarsu, wadda suka samu bisa ga umarnin
10 Da suka kai Gelilot kusa da Urdun cikin ƙasar Kan’ana, sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka gina bagade a can, a Urdun. 11 Sa’ad da Isra’ilawa suka ji cewa sun gina bagade a iyakar Kan’ana, a Gelilot kusa da Urdun wajen gefensu na Isra’ilawa, 12 sai dukan Isra’ilawa suka taru a Shilo don su je su yaƙe su.
13 Saboda haka sai Isra’ilawa suka aiki Finehas ɗan Eleyazar, firist, zuwa ƙasar Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse. 14 Suka aiki shugabanni guda goma su tafi tare da shi, ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila, kowannensu shugaba ne a iyalansa.
15 Sa’ad da suka je Gileyad, wurin mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, sai suka ce musu, 16 “Dukan jama’ar
21 Sai mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka amsa wa shugabannin iyalan Isra’ila suka ce, 22 “Maɗaukaki, Allah,
24 “A’a! Mun yi haka ne don tsoro, kada nan gaba ’ya’yanku su ce wa ’ya’yanmu, ‘Me ya haɗa ku da
26 “Shi ya sa muka ce, ‘Bari mu yi shiri mu gina bagade, amma ba na ƙona hadayu ko na sadaka ba.’ 27 Sai dai yă zama shaida tsakaninmu da ku, da kuma waɗanda za su zo a baya, cewa za mu yi wa
28 “Muka kuma ce, ‘In har suka ce mana, ko ’ya’yanmu haka, sai mu amsa mu ce ku dubi bagaden da yake daidai da na
29 “Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa
30 Da Finehas firist, da shugabannin mutanen, shugabannin iyalan Isra’ila, suka ji abin da mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse suka ce, sai suka ji daɗi. 31 Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse, “Yau mun san
32 Sai Finehas ɗan Eleyazar, firist, da shugabannin suka koma Kan’ana daga saduwa da mutanen Ruben da mutanen Gad a Gileyad, suka kai wa Isra’ilawa rahoto. 33 Isra’ilawa suka ji daɗin rahoton da suka ji, suka kuma yi wa Allah yabo. Ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su rushe ƙasar da mutanen Ruben da mutanen Gad suke ciki ba.
34 Sai mutanen Ruben da mutanen Gad suka ba wa wannan bagaden sunan, Shaida Tsakaninmu, cewa