1 Sa’ad da Yabin sarkin Hazor ya ji wannan, sai ya aika saƙo zuwa wurin Yobab sarkin Madon, da sarkin Shimron, da Akshaf, 2 ya kuma aika zuwa ga sarakunan arewa waɗanda suke kan tuddai da kuma waɗanda suke cikin Araba a kudancin Kinneret da cikin filayen kwari, da cikin Nafot Dor a yamma; 3 ya kuma aika zuwa ga Kan’aniyawa a gabas da yamma; da kuma zuwa ga Amoriyawa, Hittiyawa da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke kan tuddai; da kuma Hiwiyawa masu zama a gindin dutsen Hermon a yankin Mizfa. 4 Suka fito da dukan rundunansu da keken yaƙi masu yawan gaske, babbar runduna, yawansu ya yi kamar yashin bakin teku. 5 Duk sarakunan nan suka haɗa mayaƙansu tare, suka kafa sansani a bakin Ruwayen Meron don su yi yaƙi da Isra’ilawa.
6
7 Sai Yoshuwa da dukan mayaƙan suka auka musu a bakin Ruwayen Meron. 8
10 A lokacin nan Yoshuwa ya koma da baya ya ci Hazor da yaƙi, ya kuma kashe sarkinta da takobi. (Hazor ce babbar masarautan ƙasashen nan.) 11 Suka karkashe duk mazaunan ƙasar da takobi, ba su bar wani mai numfashi ba, suka kuma ƙona Hazor.
12 Yoshuwa ya ƙwace masarautun nan duka ya kuma kashe sarakunansu da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan
16 Saboda haka Yoshuwa ya cinye ƙasar duka da yaƙi, dukan Negeb, duka yankin Goshen, filayen kwari na yamma, Araba da tuddai na Isra’ila da kwarinta. 17 Daga Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa wajajen Seyir, zuwa Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon ƙasa da Dutsen Hermon. Ya kama sarakunansu ya karkashe su. 18 Yoshuwa ya daɗe yana yaƙi da dukan waɗannan sarakuna. 19 Sai Hiwiyawa kaɗai waɗanda suke zama a Gibeyon, sauran ba ko birni ɗaya da ta yi yarjejjeniya ta salama da Isra’ilawa, Isra’ilawa kuwa suka ci dukansu da yaƙi. 20 Gama
21 A lokacin nan Yoshuwa ya je ya hallaka Anakawa daga ƙasar tudu. Daga Hebron, Debir da Anab. Daga dukan ƙasar tuddai na Yahuda, da kuma dukan ƙasar tudu ta Isra’ila, Yoshuwa ya hallaka su duka da garuruwansu. 22 Ba a bar waɗansu Anakawa a harabar Isra’ila ba; sai dai a Gaza, Gat da Ashdod ne aka samu waɗanda suka ragu da rai. 23 Yoshuwa kuwa ya ƙwace dukan ƙasar yadda