1 Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yă je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi. 2 Amma sa’ad da Bikin Tabanakul na Yahudawa ya yi kusa, 3 sai ’yan’uwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi. 4 Ba wanda yake so a san shi da zai yi abu a ɓoye. Da yake kana yin waɗannan abubuwa, sai ka nuna kanka ga duniya.” 5 Domin ko ’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba.
6 Saboda haka Yesu ya ce musu,
10 Amma fa, bayan ’yan’uwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye. 11 A Bikin kuwa, Yahudawa suka yi ta nemansa, suna cewa, “Ina mutumin yake?”
12 A cikin taron kuwa aka yi ta raɗe-raɗe game da shi. Waɗansu suka ce, “Shi mutumin kirki ne.”
14 Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, sa’an nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa. 15 Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?”
16 Yesu ya amsa ya ce,
20 Taron suka amsa suka ce, “Kana da aljani, wane ne yake so yă kashe ka?”
21 Yesu ya ce musu,
25 A nan ne fa waɗansu mutane daga Urushalima suka fara tambaya suna cewa, “Ashe, ba wannan mutum ne suke nema su kashe ba? 26 Ga shi nan yana magana a fili, su kuma ba su ce masa uffam ba. Ko hukumomi sun yarda cewa shi ne Kiristi? 27 Mun dai san inda mutumin nan ya fito; amma sa’ad da Kiristi ya zo ba wanda zai san inda ya fito.”
28 Yesu yana cikin koyarwa a filin haikali ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce,
30 Da jin haka, sai suka yi ƙoƙari su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna. 31 Duk da haka, da yawa a cikin taron suka ba da gaskiya gare shi. Suka ce, “Sa’ad da Kiristi ya zo, zai yi abubuwan banmamaki fiye da na wannan mutum ne?”
32 Farisiyawa suka ji taron suna raɗe-raɗen waɗannan abubuwa game da shi. Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki masu gadin haikalin su kama shi.
33 Sai Yesu ya ce,
35 Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina mutumin nan yake niyyar tafiya da ba za mu iya samunsa ba? Zai je wurin mutanenmu da suke zaune warwatse a cikin Hellenawa, yă kuma koya wa Hellenawa ne? 36 Me yake nufi da ya ce,
37 A rana ta ƙarshe kuma mafi girma ta Bikin, Yesu ya tsaya ya yi magana da babbar murya ya ce,
40 Da jin kalmominsa, waɗansu mutane suka ce, “Ba shakka, mutumin nan shi ne Annabin.”
41 Waɗansu suka ce, “Shi ne Kiristi.”
45 A ƙarshe masu gadin haikali suka koma wurin manyan firistocin da Farisiyawa, waɗanda suka tambaye su cewa, “Don me ba ku kawo shi nan ba?”
46 Sai masu gadin suka ce, “Kai, babu wanda ya taɓa magana kamar wannan mutum.”
47 Sai Farisiyawa suka amsa cikin fushi suka ce, “Af, kuna nufi har da ku ma ya ruɗe ku ke nan? 48 Akwai wani daga cikin masu mulki ko cikin Farisiyawan da ya gaskata da shi? 49 A’a! Sai dai wannan taron da ba su san kome game da Doka ba, la’anannu ne.”
50 Nikodimus, wanda ya je wurin Yesu dā, wanda kuma yake ɗayansu ya ce, 51 “Ashe, dokarmu takan hukunta mutum ba tare da an fara ji daga bakinsa game da abin da yake yi ba?”
52 Sai suka amsa suka ce, “Kai ma daga Galili ne? Bincika ka gani, za ka iske cewa ba annabin da zai fito daga Galili.”
53 Sai kowannensu ya koma gidansa.
<- Yohanna 6Yohanna 8 ->