1 Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin. 2 Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!”
3 Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin. 4 Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin. 5 Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba. 6 Sa’an nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can, 7 haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin. 8 A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata. 9 (Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.) 10 Sai almajiran suka koma zuwa inda suke zama.
11 Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin, 12 sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu.
13 Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?”
15 Sai ya ce,
16 Yesu ya ce mata,
17 Yesu ya ce,
18 Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.
19 Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce,
21 Sai Yesu ya sāke ce musu,
24 Toma kuwa (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran sa’ad da Yesu ya zo. 25 Saboda haka sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji!”
26 Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce,
28 Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”
29 Sai Yesu ya ce masa,
30 Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba. 31 An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.
<- Yohanna 19Yohanna 21 ->