1 Da ya gama addu’a, sai Yesu ya fita tare da almajiransa suka haye Kwarin Kidron. A wancan ƙetaren kuwa akwai lambun zaitun, da shi da almajiransa suka shiga ciki.
2 To, Yahuda, wanda ya bashe shi, ya san wurin, domin Yesu ya sha zuwa wurin da almajiransa. 3 Saboda haka Yahuda ya zo cikin lambun, yana jagoranta ƙungiyar sojoji da waɗansu ma’aikata daga wurin manyan firistoci da Farisiyawa. Suna riƙe da toci, fitilu da kuma makamai.
4 Yesu kuwa, sane da duk abin da zai same shi, ya fito ya tambaye, su ya ce,
5 Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.”
7 Sai ya sāke tambayar su ya ce,
8 Yesu ya amsa ya ce,
10 Sai Siman Bitrus, wanda yake da takobi, ya zāre, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunnensa na dama (Sunan bawan kuwa Malkus ne.)
11 Sai Yesu ya umarce Bitrus ya ce,
12 Sai ƙungiyar soja tare da shugaban sojanta da kuma ma’aikatan Yahudawa suka kama Yesu. Suka daure shi 13 sa’an nan suka kawo shi da farko wurin Annas, wanda yake surukin Kayifas, babban firist a shekaran nan. 14 Kayifas ne wanda ya shawarci Yahudawa cewa zai fi kyau mutum ɗaya yă mutu saboda mutane.
15 Siman Bitrus da kuma wani almajiri suna bin Yesu. Domin almajirin nan sananne ne ga babban firist, sai ya shiga tare da Yesu a filin gidan babban firist ɗin, 16 Bitrus kuwa ya dakata a waje a bakin ƙofa. Almajirin nan da yake sananne ga babban firist, ya dawo ya yi magana da yarinyar mai aiki a can, ya kuma shigo da Bitrus.
17 Yarinyar da take bakin ƙofar ta ce wa Bitrus, “Kai ba ɗaya ne daga cikin almajiran mutumin nan ba ne?”
18 To, ana sanyi, bayi da ma’aikatan suna tsattsaye kewaye da wutar da suka hura don su ji ɗumi. Bitrus ma yana tsaye tare da su, yana jin ɗumi.
19 Ana cikin haka, sai babban firist ya tuhumi Yesu game da almajiransa da kuma koyarwarsa.
20 Yesu ya amsa ya ce,
22 Da Yesu ya faɗa haka, sai ɗaya daga cikin ma’aikatan da yake tsaye kusa ya mare shi a fuska ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”
23 Yesu ya amsa ya ce,
25 Da Siman Bitrus yana nan tsaye yana jin ɗumin wuta, sai aka tambaye shi, “Kai, kai ma ba ɗaya daga cikin almajiransa ba ne?”
26 Sai wani daga cikin bayin babban firist dangin wanda Bitrus ya sare wa kunne, ya tambaya shi ya ce, “Kana tsammani ban gan ka tare da shi a gonar zaitun ba?” 27 Bitrus ya sāke yin mūsu, nan take kuwa zakara ya yi cara.
28 Sa’an nan Yahudawa suka fitar da Yesu daga wurin Kayifas zuwa fadar gwamnar Roma. A yanzu dai, safiya ta yi, don gudu kada su ƙazantar da kansu Yahudawa ba su shiga cikin fadar ba; sun so su iya ci Bikin Ƙetarewa. 29 Saboda haka Bilatus ya fito wajensu ya ce, “Wace ƙara kuke kawowa game da mutumin nan?”
30 Suka amsa suka ce, “Da a ce shi ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bashe shi gare ka ba.”
31 Bilatus ya ce, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga dokarku.”
33 Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?”
34 Yesu ya yi tambaya ya ce,
35 Bilatus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne? Ai, mutanenka ne da kuma manyan firistoci suka bashe ka gare ni. Me ka yi?”
36 Yesu ya ce,
37 Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!”
38 Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?”
40 Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “Kai, ba shi ba! A ba mu Barabbas!” To, Barabbas ɗin nan yana da hannu dumu-dumu a wani tawaye.
<- Yohanna 17Yohanna 19 ->-
a Yoh 6.39