1 To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da ’yar’uwarta Marta. 2 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta. 3 Saboda haka ’yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, “Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya.”
4 Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce,
7 Sai ya ce wa almajiransa,
8 Sai suka ce, “Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?”
9 Yesu ya amsa ya ce,
11 Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu,
12 Almajiransa suka ce, “Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi.” 13 Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.
14 Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa,
16 Sai Toma (wanda ake kira Didaimus) ya ce wa sauran almajiran, “Mu ma mu je, mu mutu tare da shi.”
17 Da isowarsa, Yesu ya tarar Lazarus ya riga ya yi kwana huɗu a kabari. 18 Betani bai kai mil biyu ba daga Urushalima, 19 Yahudawa da yawa kuwa suka zo wurin Marta da Maryamu don su yi musu ta’aziyya, saboda rasuwar ɗan’uwansu. 20 Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita don ta tarye shi, amma Maryamu ta zauna a gida.
21 Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ubangiji, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba. 22 Amma na san cewa ko yanzu ma Allah zai ba ka duk abin da ka roƙa.”
23 Yesu ya ce mata,
24 Marta ta amsa ta ce, “Na sani zai sāke tashi a tashin matattu a rana ta ƙarshe.”
25 Yesu ya ce mata,
27 Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”
28 Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.” 29 Sa’ad da Maryamu ta ji haka sai ta yi wuf ta tafi wurinsa. 30 Yesu dai bai riga ya shiga ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana inda Marta ta tarye shi. 31 Da Yahudawan da suke tare da Maryamu a cikin gida, suke mata ta’aziyya, suka ga ta yi wuf ta fita, sai suka bi ta, suna tsammani za tă kabarin ne tă yi kuka a can.
32 Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.”
33 Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu. 34 Sai ya yi tambaya ya ce,
35 Yesu ya yi kuka.
36 Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
37 Amma waɗansunsu suka ce, “Anya, wanda ya buɗe wa makahon nan idanu, ba zai iya yin wani abu yă hana wannan mutum mutuwa ba?”
38 Yesu, har yanzu cike da juyayi, ya zo kabarin. Kogo ne da aka rufe bakin da dutse. 39 Sai Yesu ya ce,
40 Sai Yesu ya ce,
41 Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce,
43 Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce,
45 Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi. 46 Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi. 47 Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa.
49 Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba! 50 Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”
51 Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa, 52 ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro ’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya. 53 Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa.
54 Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa.
55 Sa’ad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa. 56 Suka yi ta neman Yesu, da suke a tsaitsaye a filin haikali kuwa suka dinga tambayar juna, suna cewa, “Me kuka gani? Anya, zai zo Bikin kuwa?” 57 Manyan firistoci da Farisiyawa tuni sun riga sun yi umarni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, yă faɗa don su kama shi.
<- Yohanna 10Yohanna 12 ->