Duk da haka kina da irin kallon da karuwa takan yi;
kin ƙi ki ji kunya.
4 Yanzu ba kin kira ni,
‘Mahaifina, abokina daga ƙuruciyata ba,
5 kullum za ka riƙa fushi?
Hasalarka za tă ci gaba har abada ne?’
Haka kike magana,
amma kina aikata dukan muguntar da kika iya yi.”
Isra’ila marar aminci
6 A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can. 7 Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za tă komo wurina amma ba tă yi haka ba, ’yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani. 8 Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina. 9 Domin fasikancin Isra’ila bai yi tasiri gare ta ba, sai ta ƙazantar da ƙasar ta kuma yi zina da dutse da kuma itace. 10 Duk da wannan duka, Yahuda ’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce,” in ji Ubangiji.
11Ubangiji ya ce mini, “Isra’ila marar bangaskiya ta fi Yahuda marar aminci. 12 Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa,
“ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji,
‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba,
gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji,
‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.
13 Ki dai yarda da laifinki
kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye,
kin watsar da alheranki ga baƙin alloli
a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa,
ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ ”
in ji Ubangiji.
14 “Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona. 15 Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi. 16 A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba. 17 A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba. 18 A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo.
19 “Ni kaina na faɗa,
“ ‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ’ya’yana maza
in ba ki ƙasa mai daɗi,
gādo mafi kyau da wata al’umma.’
Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’
ba za ki ƙara rabuwa da bina ba.
20 Amma kamar mace marar aminci ga mijinta,
haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,”