1 Da firist nan Fashhur ɗan Immer, babban ma’aikaci a cikin haikalin Ubangiji, ya ji Irmiya yana annabcin waɗannan abubuwa, 2 sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka aka kuma sa shi a turu a Ƙofar Bisa na Benyamin a haikalin Ubangiji. 3 Kashegari, sa’ad da Fashhur ya fitar da shi daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashhur ba, amma ya ba ka suna Magor-Missabib.[a]4 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi. 5 Zan ba wa abokan gābansu dukan dukiyar wannan birni dukan amfaninsa, dukan abubuwa masu daraja na sarakunan Yahuda. Za su kwashe su ganima su kai su Babilon. 6 Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ”