1 Mutanen Isra’ila sun riga sun yi rantsuwa a Mizfa cewa, “Ba ɗayanmu da zai ba da ’yarsa aure ga mutumin Benyamin.”
2 Sai mutanen suka tafi Betel,[a] inda suka zauna a gaban Allah har yamma, suna tā da muryoyinsu suna kuka mai zafi. 3 Suka ce, ya
4 Kashegari da sassafe mutane suka gina bagade suka miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama.
5 Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban
6 To, Isra’ilawa suka yi juyayin ’yan’uwansu, mutanen Benyamin. “Yau an hallaka kabila daga cikin Isra’ila. 7 Yaya za mu ba wa waɗanda suka rage mata, da yake mun riga mun yi rantsuwa a gaban
10 Saboda haka sai taron ya umarci jarumai dubu goma sha biyu su je Yabesh Gileyad su karkashe waɗanda suke zaune a can, duk da mata da yara. 11 Suka ce musu, “Ga abin da za ku yi. Ku karkashe duk namiji da kowace macen da ta riga ta san namiji.” 12 Suka samu a cikin mutanen da suke zaune a Yabesh Gileyad mata ɗari huɗu da ba su taɓa kwana da namiji ba, suka kwashe su zuwa sansani a Shilo a Kan’ana.
13 Sa’an nan dukan taro suka aika wa mutanen Benyamin da suke a Dutsen Rimmon cewa yaƙi ya ƙare, yanzu sai salama. 14 Saboda haka mutanen Benyamin suka komo a lokacin aka kuma ba su matan Yabesh Gileyad nan da aka bari da rai. Amma matan ba su ishe su duka ba.
15 Mutanen kuwa suka yi juyayi saboda mutanen Benyamin, domin
20 Saboda haka suka cewa mutanen Benyamin, “Ku je ku ɓuya a gonakin inabi 21 ku lura. Sa’ad da ’yan matan Shilo suka fito waje don su yi rawa, ku fito a guje daga gonakin inabi, kowannenku yă kama wa kansa mata daga cikin ’yan matan Shilo, ku tafi ƙasar Benyamin. 22 Sa’ad da iyayensu maza ko ’yan’uwansu suka kawo mana ƙara, za mu ce musu, ‘Ku yi mana alheri ku bar su, domin ba mu samo musu mata ba lokacin yaƙi, ku kuma marasa laifi ne, tun da yake ba ku ba da ’ya’yan matanku gare su ba.’ ”
23 Haka mutanen Benyamin suka yi. Yayinda ’yan matan suke rawa, kowane mutum ya kama ɗaya ya yi gaba da ita ta zama matarsa. Sa’an nan suka komo ƙasar gādonsu suka sāke giggina garuruwan suka kuwa zauna a cikinsu.
24 A lokacin, Isra’ilawa sun bar wurin suka tafi gida zuwa ga kabilansu da zuriyoyinsu, kowane zuwa gādonsa.
25 A kwanakin Isra’ila ba ta da sarki; kowa ya yi abin da ya ga dama.
-
a Ko kuwa zuwa gidan Allah
Languages