11
Reshe daga Yesse
1 Toho zai fito daga kututturen Yesse;
daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.
2 Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa,
Ruhun hikima da na fahimta,
Ruhun shawara da na iko,
Ruhun sani da na tsoron Ubangiji ,
3 zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji .
Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba,
ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;
4 amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a,
da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya.
Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa;
da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.
5 Adalci ne zai zama abin ɗamararsa
aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.
6 Kyarkeci zai zauna tare da ɗan rago
damisa za tă kwanta tare da akuya,
ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare;
ɗan yaro ne zai lura da su.
7 Saniya da beyar za su yi kiwo tare,
ƙananansu za su kwanta tare,
zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya.
8 Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa,
ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi.
9 Ba za su yi lahani ko su hallaka
wani a dutsena mai tsarki ba,
gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji
kamar yadda ruwaye suka rufe teku.
10 A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja. 11 A wannan rana Ubangiji zai miƙa hannunsa sau na biyu don yă maido da raguwar da ta rage na mutanensa daga Assuriya, daga Masar ta Ƙasa, daga Masar ta Bisa,[a] daga Kush,[b] daga Elam, daga Babiloniya,[c] daga Hamat da kuma daga tsibiran teku.
12 Zai tā da tuta saboda al’ummai
yă kuma tattara masu zaman bauta na Isra’ila;
zai tattara mutanen Yahuda da suke a warwatse
kusurwoyi huɗu na duniya.
13 Kishin Efraim zai ɓace,
za a kuma kau da abokan gāban Yahuda;
Efraim ba zai yi kishin Yahuda ba,
haka ma Yahuda ba zai yi gāba da Efraim ba.
14 Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma;
tare za su washe mutane wajen gabas.
Za su ɗibiya hannuwa a kan Edom da Mowab,
Ammonawa kuma za su yi musu biyayya.
15 Ubangiji zai busar da
bakin tekun Masar;
da iska mai zafi zai share hannunsa
a bisa Kogin Yuferites[d]
Zai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwai
saboda mutane su iya hayewa da ƙafa.
16 Za a yi babbar hanya saboda raguwa mutanensa
da ta rage daga Assuriya,
kamar yadda ta kasance wa Isra’ila