28 Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.
Mutuwar Yaƙub
29 Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti, 30 kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti. 31 A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu. 32 Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa.”[n]
33 Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga ’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.
aYahuda ya yi kamar ya fito daga Ibraniyanci na yabo ne.bKo kuwa sai Shilo ya zo; ko kuwa sai ya zo ga girma ya dace.cKo kuwa zai zama marar walƙiya daga ruwan inabi, haƙorarsa farare daga madaradKo kuwa mai ƙarfieKo kuwa sansanin wutaf Dan a nan yana nufin yakan tanada adalci.
g Gad na iya nufin fāɗawa da kuma ƙungiyar mahara.
hKo kuwa yakan faɗa kyawawan kalmomiiKo kuwa Yusuf aholakin jeji ne, aholakin jeji kusa da rafi, jakin jeji a tudun mai kunyoyijKo kuwa mahara za su fāɗa, za su harba, za su rage, za su tsayakDa Ibraniyanci ShaddailKo kuwa kakana, mai girma kamarmKo kuwa wanda aka raba danKo kuwa ’ya’ya mazan Het