Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne;
a ranar da aka halicce ka an shirya su.
14 An shafe ka kamar kerub mai tsaro,
gama haka na naɗa ka.
Kana a tsattsarkan dutsen Allah;
ka yi tafiya a tsakiyar duwatsun wuta.
15 Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka
daga ranar da aka halicce ka
sai da aka sami mugunta a cikinka.
16 Ta wurin yawan kasuwancinka
ka cika da rikici,
ka kuma yi zunubi.
Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah,
na kore ka, ya kerub mai tsaro,
daga cikin duwatsun wuta.
17 Zuciyarka ta cika da alfarma
saboda kyanka,
ka kuma lalace hikimarka
saboda darajarka.
Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa;
na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna.
18 Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta
ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka.
Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka,
ta cinye ka,
na maishe ka toka a bisa ƙasa
a kan idon dukan waɗanda suke kallonka.
19 Dukan al’umman da suka san ka
sun giggice saboda masifar da ta auko maka;
ka zo ga mummunar ƙarshe
ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.’ ”
Annabci a kan Sidon
20 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 21 “Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon; ka yi annabci a kanta 22 ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Ina gāba da ke, ya Sidon,
zan sami ɗaukaka a cikinki.
Za su san cewa ni ne Ubangiji,
sa’ad da na zartar da hukunci a kanta
na kuma nuna kaina mai tsarki a cikinta.
23 Zan aika da annoba a kanta
in kuma sa jini ya zuba a titunanta.
Kisassu za su fāɗi a cikinta,
da takobi yana gāba da ita a kowane gefe.
Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.
24 “ ‘Mutanen Isra’ila ba za su ƙara kasance da mugayen maƙwabta waɗanda za su zama sarƙaƙƙiya masu zafi da ƙaya mai tsini ba. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka.
25 “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da na tattara mutanen Isra’ila daga al’ummai inda suke a warwatse, zan nuna kaina mai tsarki a cikinsu a idon al’ummai. Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu, wadda na ba wa bawana Yaƙub. 26 Za su zauna a can lafiya su kuma gina gidaje su nome gonakin inabi; za su zauna lafiya sa’ad da zan zartar da hukunci a kan dukan maƙwabtansu da suka wulaƙanta su. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji Allahnsu.’ ”