1 Sa’an nan
6 “Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar tabanakul, da Tentin Sujada; 7 ka ajiye daron tsakanin Tentin Sujada da bagaden, ka kuma zuba ruwa a cikinsa. 8 Ka yi fili kewaye da shi, ka kuma sa labule a ƙofar shiga filin.
9 “Ka ɗauki man shafewa ka shafe tabanakul da duka abin da yake cikinsa; ka keɓe shi da dukan kayayyakinsa, zai zama tsarkake. 10 Sa’an nan ka shafe bagaden hadaya ta ƙonawa da kayansa; ka keɓe bagaden, zai zama mai tsarki. 11 Ka shafe daron da wurin ajiyarsa, ka kuma keɓe su.
12 “Ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka wanke su da ruwa. 13 Sa’an nan ka sa wa Haruna tsarkakun riguna, ka shafe shi, ka kuma keɓe shi don yă yi mini hidima a matsayin firist. 14 Ka kawo ’ya’yansa maza ka sa musu taguwoyi. 15 Ka shafe su yadda ka shafe mahaifinsu, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Shafe musu man, zai sa su zama firistoci na ɗinɗinɗin, dukan zamanansu.” 16 Musa ya aikata dukan kome yadda
17 Da haka aka kafa tabanakul, a rana ta fari ga wata na fari a shekara ta biyu. 18 Sa’ad da Musa ya kafa tabanakul, ya sa rammuka a wurinsu, ya sa katakan, ya kuma sa sandunan, ya kakkafa dogayen sandunan. 19 Sa’an nan ya shimfiɗa tentin a bisa tabanakul, ya kuma sa murfi a bisa tentin, yadda
20 Ya ɗauki dokokin Alkawari ya sa a cikin akwatin, ya kuma zura sandunan a zoban akwatin, sa’an nan ya sa murfin kafara a bisansa. 21 Sai ya kawo akwatin a cikin tabanakul, ya kuma rataye labulen rufewa ya tsare akwatin Alkawarin, yadda
22 Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen. 23 Ya shirya burodin a kai a gaban
24 Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul 25 ya kuma shirya fitilun a gaban
26 Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen 27 ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda
28 Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul. 29 Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda
30 Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki, 31 a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu. 32 Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda
33 Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin.
34 Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar
36 Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul. 37 Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi. 38 Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.