1 Ka lura da matakanka sa’ad da ka tafi gidan Allah. Ka je kusa don ka saurara a maimakon miƙa hadaya kamar wawaye, waɗanda ba su san sun yi laifi ba.
4 Sa’ad da ka yi alkawari ga Allah, kada ka ɓata lokaci wajen cika shi. Ba ya jin daɗin wawaye; ka cika alkawarinka. 5 Gara kada ka yi alkawari, da ka yi amma ba ka cika ba. 6 Kada ka bar bakinka ya kai ga yin zunubi. Kada kuma ka kai ƙara wurin ɗan saƙon haikali cewa, “Alkawarin da na yi kuskure ne.” Me ya sa Allah yake fushi a kan abin da ka faɗa har yă lalatar da aikin hannuwanka? 7 Yawan buri da yawan magana ba su da amfani. Saboda haka, ka ji tsoron Allah.
8 In ka ga ana zaluntar matalauta a wani yanki, ba a yin adalci, ana kuma tauye hakki, kada ka yi mamakin waɗannan abubuwa; domin akwai wani jami’in da yake bisa da wani, a bisansu biyu kuwa akwai wani. 9 Kowa yakan amfana da bunkasar amfanin ƙasa, sarki kansa yana samun riba daga gonaki.
13 Na ga wani mugun abu a duniya,
16 Wannan ma mugun abu ne,
18 Sa’an nan na gane cewa abu mai kyau ne, daidai ne kuma mutum yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗin aikin da ya yi a ’yan kwanakin da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum daga faman wahalarsa a duniya a cikin ’yan kwanakin da Allah ya ba shi a duniya, gama wannan shi ne rabonsa. 19 Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah. 20 Da ƙyar yake tunani a kan kwanakin rayuwarsa, domin Allah ya yarje masa, yă zauna da farin ciki.
<- Mai Hadishi 4Mai Hadishi 6 ->