8
Kwandon nunannun ’ya’yan itace
1 Ga abin da 
Sai na amsa na ce, “Kwandon nunannun ’ya’yan itace.” 
Sai Ubangiji  ya ce mini, “Lokaci ya yi wa mutanena Isra’ila da ba zan ƙara barinsu ba.
3 “A ranan nan,” in ji 
 4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata 
kuka kori matalautan ƙasar.
5 Kuna cewa,
“Yaushe Sabon Wata zai wuce 
don mu sayar da hatsi, 
Asabbaci ta wuce, 
don mu sayar da alkama?” 
Mu yi awo da ma’aunin zalunci 
mu ƙara kuɗin kaya 
mu kuma cutar da mai saya, 
 6 mu sayi matalauta da azurfa 
masu bukata kuma da takalmi, 
mu sayar da alkamar haɗe da yayi.
7 
 8 “Shin, ƙasar ba za tă yi rawan jiki saboda wannan ba, 
kuma duk masu zama a cikinta ba za su yi makoki ba? 
Ƙasar duka za tă hau ta sauka kamar Nilu; 
za a dama ta sa’an nan ta nutse 
kamar kogin Masar.
9 “A wannan rana,” in ji 
“Zan sa rana ta fāɗi da tsakar rana 
in kuma duhunta duniya da rana tsaka. 
 10 Zan mai da bukukkuwanku na addini su zama makoki 
kuma dukan waƙoƙinku su zama kuka. 
Zan sa dukanku ku sa rigunan makoki 
za ku kuma aske kawunanku. 
Zan sa wannan lokaci yă zama kamar lokacin da ake makokin ɗan tilon da ake da shi 
kuma ƙarshenta kamar rana mai ɗaci. 
 11 “Ranakun suna zuwa,” in ji Ubangiji  Mai Iko Duka, 
“sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar, 
ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba, 
sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji . 
 12 Mutane za su yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku 
suna yawo daga arewa zuwa kudu, 
suna neman maganar Ubangiji , 
amma ba za su samu ba.
13 “A wannan rana
“kyawawan ’yan mata da kuma samari masu ji da ƙarfi 
za su suma don ƙishirwa. 
 14 Waɗanda suka yi rantsuwa da abin kunya[b] na Samariya, 
ko kuma su ce, ‘Muddin allahnku yana a raye, ya Dan,’ 
ko kuwa, ‘Muddin allahn[c] Beyersheba yana a raye,’ 
za su fāɗi, 
 Languages
Languages