3
An kira shaidu a kan Isra’ila
1 Ku ji wannan maganar da
2 “Ku ne kaɗai na zaɓa
cikin dukan al’umman duniya;
saboda haka zan hukunta ku
saboda dukan zunubanku.”
3 Mutum biyu za su iya yin tafiya tare
in ba su yarda su yi haka ba?
4 Zaki yakan yi ruri a jeji
in bai sami kama nama ba?
Zai yi gurnani a cikin kogonsa
in bai kama kome ba?
5 Tsuntsu yakan fāɗa a tarko a ƙasa
inda ba a sa tarko ba,
ko tarko yakan zargu daga ƙasa
in ba abin da ya taɓa shi?
6 Idan aka busa ƙaho a ciki birni
mutane ba sa yin rawar jiki?
Sa’ad da bala’i ya auko wa birni,
ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?
7 Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu
ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.
8 Zaki ya yi ruri,
wa ba zai tsorata ba?
wa ba zai yi annabci ba?
9 Ku yi shela ga kagarun Ashdod
da kuma ga kagarun Masar.
“Ku tara kanku a tuddan Samariya;
ku ga rashin jituwar da take a cikinta,
da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”
10 “Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,”
in ji Ubangiji ,
“sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”
11 Saboda haka ga abin da
“Abokin gāba zai ƙwace ƙasar,
zai saukar da mafakarku,
zai washe kagarunku.”
12 Ga abin da
“Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki
ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya,
haka za a ceci Isra’ilawa,
masu zama a Samariya
da kan gado kawai
da kuma a ɗan ƙyalle[a] a kan dogayen kujerunsu.[b]”
13 “Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji
14 “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta,
zan hallaka bagadan Betel;
za a yayyanka ƙahonin bagadan
za su fāɗa ƙasa
15 Zan rushe gidan rani
da na damina;
gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su
haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,”
Languages