1 Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan ’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi.
2 Sarki ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo waɗannan?”
3 Sai sarki ya ce, “Ina jikar maigidanka?”
4 Sai sarki ya ce wa Ziba, “Duk abin da yake na Mefiboshet, ya zama naka.”
5 Yayinda Sarki Dawuda ya kusato Bahurim, sai ga wani mutumin dangin Shawulu ya fito daga can, sunansa Shimeyi ɗan Gera. Ya fito yana ta la’anta yayinda yake fitowa. 6 Ya jajjefi Dawuda da dukan fadawan sarki da duwatsu, ko da yake sojoji da masu gadin sarki na musamman suna kewaye da sarki dama da hagu. 7 Yayinda yake la’antar, Shimeyi ya ce, “Tafi daga nan, tafi daga nan, mai kisankai, mutumin banza kawai! 8
9 Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce wa sarki, “Ranka yă daɗe, don me wannan mataccen kare yake la’antarka? Bari in je in datse kansa.”
10 Amma sarki ya ce, “Ba ruwana da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya. Idan yana la’ana ne domin
11 Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abishai da dukan fadawansa, “Ɗana, na cikina, yana ƙoƙari yă kashe ni. Balle wannan mutumin Benyamin! Ku ƙyale shi, yă yi ta zargi,
13 Saboda haka Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu yayinda Shimeyi yana tafiya ɗaura da shi a gefen tudu, yana zagi, yana jifansa da duwatsu, yana tayar masa da ƙura. 14 Sarki da dukan mutanen da suke tare da shi suka isa masauƙinsu a gajiye. A can fa ya huta.
15 Ana cikin haka, Absalom da dukan Isra’ila suka iso Urushalima, Ahitofel kuwa yana tare da shi. 16 Sai Hushai mutumin Arkitawa, abokin Dawuda ya je wurin Absalom ya ce masa, “Ran sarki yă daɗe! Ran sarki yă daɗe!”
17 Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake nuna wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”
18 Hushai ya ce wa Absalom, “A’a, ai, wanda
20 Absalom ya ce wa Ahitofel, “Ba mu shawararka. Me za mu yi?”
21 Ahitofel ya ce wa Absalom, “Je ka kwana da ƙwarƙwaran mahaifinka waɗanda ya bari su lura da fada. Ta haka dukan Isra’ila za su ji cewa ka mai da kanka abin wari a hancin mahaifinka, dukan hannuwan waɗanda suke tare da kai kuwa za su sami ƙarfi.” 22 Saboda haka suka kafa wa Absalom tenti a bisa rufin ɗaki, a can ya kwana da ƙwarƙwaran mahaifinsa a gaban dukan Isra’ila.
23 To, a kwanakin nan shawarar da Ahitofel yakan bayar takan zama kamar wadda aka nemi daga Allah ne. Haka Dawuda da Absalom duk suke ɗaukan dukan shawarar Ahitofel.
<- 2 Sama’ila 152 Sama’ila 17 ->