1 A shekara ta bakwai ta Yehu, Yowash ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima na tsawon shekaru arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; daga Beyersheba. 2 Yowash ya aikata abin da yake daidai a idon
4 Yowash ya ce wa firistoci, “Ku tattara dukan kuɗin da ake kawo a matsayin hadayu masu tsarki na haikalin
6 Amma har zuwa shekara ta ashirin da uku ta mulkin Yowash, firistocin ba su yi gyara haikalin ba. 7 Saboda haka Sarki Yowash ya kira Yehohiyada firist da sauran firistoci ya tambaye su ya ce, “Me ya sa ba kwa gyaran abubuwan da suka lalace a haikali? Kada ku sāke karɓan kuɗi daga masu ajiya, amma a miƙa su domin gyaran haikali.” 8 Firistoci suka yarda cewa ba za su sāke karɓan kuɗi daga mutane ba, kuma ba za su yi gyaran haikalin da kansu ba.
9 Yehohiyada firist ya ɗauki akwatin ya huda rami a murfinsa. Ya ajiye shi kusa da bagade a hannun dama na haikalin
13 Ba a yi amfani da kuɗin da aka kawo a haikali don yin manyan kwanonin azurfa, lagwani, abin yayyafa ruwa, kakaki ko wani abu na zinariya, ko na azurfa domin haikalin
17 A wannan lokaci, Hazayel sarkin Aram ya haura, ya kai wa Gat hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Sa’an nan ya juya don yă yaƙi Urushalima. 18 Amma Yowash sarkin Yahuda ya kwashe tsarkakan kayan da kakanninsa, Yehoshafat, Yehoram da Ahaziya, sarakunan Yahuda suka keɓe, da kyautai da shi kansa ya keɓe, da kuma dukan azurfan da aka samu a ɗakunan ajiya haikalin
19 Game da sauran ayyukan mulkin Yowash da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 20 Hafsoshinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a Bet Millo, a kan hanyar da ta gangara zuwa Silla. 21 Hafsoshin da suka kashe shi kuwa su ne Yozabad ɗan Shimeyat da Yehozabad ɗan Shomer. Ya mutu, aka kuma binne shi tare da kakanninsa a Birnin Dawuda. Sai Amaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
<- 2 Sarakuna 112 Sarakuna 13 ->
Languages