1 Sa’ad da dukan aikin da Solomon ya yi domin haikalin
2 Sa’an nan Solomon ya tattara zuwa Urushalima dattawan Isra’ila, dukan kawunan kabilu da manyan iyalan Isra’ilawa, don su haura da akwatin alkawarin
4 Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka iso, Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin, 5 suka haura da akwatin alkawarin da kuma Tentin Sujada da dukan kayayyaki masu tsarkin da yake cikinta. Firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, suka ɗauke su; 6 Sarki Solomon kuwa da taron Isra’ila gaba ɗaya da suka taru kewaye da shi suna a gaban akwatin alkawarin, suna miƙa tumaki da shanu masu yawa da suka wuce ƙirge ko lissafi.
7 Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin
11 Sa’an nan firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki. Dukan firistocin da suke can sun tsarkake kansu, ko daga wace ɓangarori suka fito. 12 Dukan Lawiyawa waɗanda suke mawaƙa, Asaf, Heman, Yedutun da ’ya’yansu maza da dangoginsu, suka tsaya a gefen gabas na bagaden, saye da lilin mai kyau suna kuma kaɗa ganguna, garayu da molaye. Tare da su akwai firistoci 120 masu busan ƙahoni. 13 Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga