1 Yosiya ya yi Bikin Ƙetarewa ga
5 “Ku tsaya a tsattsarkan wuri, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin ’yan’uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa. 6 Ku yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku kuma shirya raguna domin ’yan’uwanku, kuna yin abin da
7 Yosiya ya tanada wa dukan mutanen da ba firistoci ba ne waɗanda suke a wurin, tumaki da awaki dubu talatin don a yanka saboda hadayun Bikin Ƙetarewa, ya kuma ba su shanu dubu uku. Dukan dabbobin kuwa daga garken sarki ne.
8 Fadawansa su ma suka ba da taimako da yardar rai ga mutane da kuma firistoci da Lawiyawa. Hilkiya, Zakariya da Yehiyel masu aiki a haikalin Allah, suka ba firistoci hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyu da ɗari shida da kuma shanu ɗari uku. 9 Haka kuma Konaniya tare da Shemahiya da Netanel, ɗan’uwansa, da Hashabiya, Yehiyel da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, suka tanadar da hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyar da kuma bijimai ɗari biyar domin Lawiyawa.
10 Sa’ad da aka shirya kome don Bikin Ƙetarewar, sai Firistoci tare da Lawiyawa suka tsaya wurin tsayawarsu bisa ga umarnin sarki. 11 Aka yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, firistoci kuma suka yayyafa jinin da aka ba su, yayinda Lawiyawa suna fiɗan dabbobi. 12 Suka keɓe hadayun ƙonawa don su ba da su ga ƙungiyoyin iyalan mutane don su miƙa ga
15 Mawaƙa zuriyar Asaf, suna a wuraren da Dawuda, Asaf, Heman da Yedutun mai duba na sarki suka tsara. Bai zama lalle matsaran ƙofofi a kowace ƙofa su bar wuraren aikinsu ba, domin ’yan’uwansu Lawiyawa sun yi shiri dominsu.
16 Ta haka fa aka yi dukan hidimar
20 Bayan wannan duka, sa’ad da Yosiya ya shirya haikali, Neko sarkin Masar ya haura don yă yi yaƙi a Karkemish a Yuferites, sai Yosiya ya fita don yă fafata da shi a yaƙi. 21 Amma Neko ya aiki ’yan saƙo ga Yosiya, yana cewa, “Me ya gama ni da kai, ya Sarkin Yahuda? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da gidan da yake gāba da ni! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada yă hallaka ka.”
22 Yosiya fa, bai juya daga gare shi ba, amma ya ɓad da kama don yă yi yaƙin. Bai saurari abin da Neko ya faɗa bisa ga umarnin Allah ba, amma ya tafi ya yaƙe shi a filin Megiddo.
23 Maharba suka harbi Yosiya, sai ya ce wa hafsoshinsa, “Ku ɗauke ni ku fita da ni daga nan; gama an yi mini mummunan rauni.” 24 Saboda haka suka ɗauke shi a keken yaƙin, suka fitar da shi, suka sa shi a wata keken yaƙin da yake da shi, suka kawo shi Urushalima, inda ya mutu. Aka binne shi a makabartar kakanninsa, sai dukan Yahuda da Urushalima suka yi makoki dominsa.
25 Annabin Irmiya ya tsara waƙoƙin makoki domin Yosiya, wanda har wa yau mawaƙa maza da mata suke rera game da Yosiya. Suka sa waɗannan su zama al’ada a Isra’ila, suna kuma a rubuce cikin Littafin Makoki.
26 Sauran ayyukan mulkin Yosiya da kuma kyawawan abubuwan da ya yi, bisa ga abin da aka rubuta a Dokar