1 A shekara ta bakwai Yehohiyada ya nuna ƙarfinsa. Ya yi alkawari da shugabanni na ɗari-ɗari, Azariya ɗan Yeroham, Ishmayel ɗan Yehohanan, Azariya ɗan Obed, Ma’asehiya ɗan Adahiya, da Elishafat ɗan Zikri. 2 Suka ratsa cikin Yahuda suka tattara Lawiyawa da shugabannin iyalan Isra’ilawa daga dukan garuruwa. Sa’ad da suka zo Urushalima, 3 dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah.
8 Lawiyawa da dukan mutanen Yahuda suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowanne ya ɗauki mutanensa, waɗanda suke aiki a Asabbaci da waɗanda suka gama aiki, gama Yehohiyada firist bai bar waɗansu ɓangarori ba. 9 Sa’an nan ya ba shugabannin māsu da garkuwoyi manya da ƙanana na sarki Dawuda, waɗanda suke cikin haikalin Allah. 10 Ya kuma sa dukan mutane, kowanne da makaminsa a hannunsa, kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikali.
11 Yehohiyada da ’ya’yansa maza suka fitar da ɗan sarki suka sa rawani a kansa; suka miƙa masa alkawarin, suka kuma yi shelarsa a matsayin sarki. Suka shafe shi suka kuma tā da murya suna cewa, “Ran sarki yă daɗe!”
12 Sa’ad da Ataliya ta ji surutun mutane suna gudu suna yabon sarki, sai ta tafi wurinsu a haikalin
14 Yehohiyada firist ya fito da shugabanni waɗanda suke shugabancin rundunar sojoji, ya ce musu, “Ku fitar da ita tsakanin sojoji ku kuma kashe duk wanda ya bi ta da takobi.” Gama firist ya ce, “Kada ku kashe ta a haikalin
16 Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari cewa shi da mutane da kuma sarki za su zama mutanen
18 Sa’an nan Yehohiyada ya sa aikin lura da haikalin
20 Ya ɗauki shugabannin ɗari-ɗari, manyan gari, shugabannin mutane da dukan mutanen ƙasar tare da shi ya saukar da sarki daga haikalin