1 Mutanen Urushalima suka mai da Ahaziya, autan Yehoram, sarki a madadinsa, da yake ’yan hari, waɗanda suka zo tare da Larabawa cikin sansani, sun kashe dukan manyan ’ya’yansa. Saboda haka Ahaziya ɗan Yeroham sarkin Yahuda ya fara mulki.
2 Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara guda. Sunan mahaifiyarsa Ataliya ce, jikanyar Omri.
3 Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau. 4 Ya aikata mugayen ayyuka a gaban
7 Ta wurin ziyarar Yoram, Allah ya kawo fāɗuwar Ahaziya. Sa’ad da Ahaziya ya iso, ya tafi tare da Yoram domin yă sadu da Yehu ɗan Nimshi, wanda
10 Sa’ad da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga cewa ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta hallaka dukan ’yan gidan sarautar Yahuda. 11 Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yehoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya ta sace shi daga cikin ’ya’yan gidan sarauta waɗanda ake shiri a kashe, ta sa shi tare da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba ’yar sarki Yoram, matar Yehohiyada firist, ta yi, gama ita ’yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya tă kashe shi. 12 Ya kasance a ɓoye tare da su a haikalin Allah shekara shida, yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.
<- 2 Tarihi 212 Tarihi 23 ->