2 Dawuda ya ce, “Kai da kanka za ka ga abin da bawanka zai yi.”
3 Sama’ila dai ya riga ya rasu, dukan Isra’ila suka yi makokinsa suka binne shi a garinsa a Rama. Shawulu kuma ya kori duk masu duba da masu maitanci daga ƙasar.
4 Filistiyawa suka tattaru suka yi sansani a Shunem. Shawulu ya tattara dukan Isra’ila suka yi sansani a Gilbowa. 5 Da Shawulu ya ga sojojin Filistiyawa sai ya ji tsoro, ya firgita ƙwarai. 6 Ya nemi nufin
8 Sai Shawulu ya sa waɗansu tufafi ya ɓad da kama, shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare, ya ce mata, “Ki yi mini duba ta hanyar sihiri, ki hawar mini duk wanda zan faɗa miki.”
9 Amma matar ta ce masa, “Tabbatacce ka dai san abin da Shawulu ya yi, ya karkashe masu duba da masu maitanci a ƙasar. Me ya sa kake sa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”
10 Shawulu ya rantse mata da
11 Sai matar ta ce, “Wa kake so in hauro maka?”
12 Da matar ta ga Sama’ila sai ta yi ihu da ƙarfi ta ce wa Shawulu, “Me ya sa ka ruɗe ni? Kai ne Shawulu!”
13 Sai sarki ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Me kika gani?”
14 Ya ce, “Yaya kamanninsa yake?”
15 Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Don me ka dame ni, ta wurin hauro da ni?”
16 Sama’ila ya ce, “Don me kake tambayata bayan
20 Da jin maganar Sama’ila sai Shawulu ya faɗi ƙasa warwas. Tsoro ya kama shi ƙwarai. Ba shi kuma da ƙarfi domin bai ci kome ba dukan yini da kuma dukan dare.
21 Da matar ta zo wurin Shawulu, ta ga shi a firgice, sai ta ce masa, “Duba baranyarka ta yi maka biyayya ta yi kasai da ranta, ta yi abin da ka ce ta yi. 22 To, kai ma ka kasa kunne ga baranyarka, zan ba ka abinci ka ci don ka sami ƙarfin tafiya.”
23 Sai ya ƙi. Ya ce, “Ba zan ci abinci ba.”
24 Matar kuwa tana da maraƙin da take kiwo a gida, sai ta ɗauke shi nan da nan ta yanka. Ta ɗauki garin fulawa ta kwaɓa, ta yi waina marar yisti. 25 Sai ta kawo wa Shawulu da bayinsa suka kuwa ci. A daren nan suka tashi suka tafi.
<- 1 Sama’ila 271 Sama’ila 29 ->