2 Shawulu kuwa na zaune a gindin itacen rumman a bayan garin Gibeya a Migron. Tare da shi akwai mutum wajen ɗari shida. 3 A cikinsu akwai Ahiya sanye da efod. Shi yaron Ikabod ɗan’uwan Ahitub ne, ɗan Finehas, ɗan Eli, firist na
4 A kowane gefe na mashigin da Yonatan ya so yă bi zuwa wurin Filistiyawa, akwai hawa mai tsawo, ana kira ɗaya Bozez, ɗayan kuma ana kira Senet. 5 Hawan da yake arewa yana fuskantar Mikmash, wanda yake kudu kuma yana fuskantar Geba.
6 Yonatan ya ce wa saurayin mai ɗaukan makamai, “Zo mu haye zuwa mashigin mutane marasa kaciyan nan, wataƙila
7 Mai ɗaukan makaman ya ce, “Ka yi duk abin da yake zuciyarka. Ci gaba, ina tare da kai gaba da baya.”
8 Yonatan ya ce, “To, zo mu haye zuwa wajen mutanen, mu sa su gan mu. 9 In suka ce mana, ‘Ku tsaya nan har mu zo wurinku,’ za mu dakata inda muke, ba za mu haura wajensu ba. 10 Amma in suka ce mana, ‘Ku haura wurinmu,’ to, sai mu haura, wannan zai zama mana alama cewa
11 Sai suka nuna kansu a sansanin Filistiyawa. Sai Filistiyawa suka ce, “Ku duba ga Ibraniyawa suna fitowa daga cikin ramummuka inda suka ɓuya.” 12 Mutanen da suke sansanin suka kira Yonatan da mai ɗaukan makamansa da babbar murya suka ce, “Ku hauro wajenmu, mu kuwa za mu koya muku hankali.”
13 Sai Yonatan ya hau dutsen da rarrafe, mai ɗaukan makamansa kuwa yana biye. Yonatan ya yi ta fyaɗa Filistiyawa da ƙasa, mai ɗaukan makamansa kuma ya yi ta karkashe su. 14 A wannan karo na farko Yonatan da mai ɗaukan makamansa suka kashe mutum wajen ashirin a wani fili mai fāɗi rabin kadada.
15 Sai tsoro ya kama dukan sojojin Filistiyawa, waɗanda suke cikin sansanin da waɗanda suke fili, har da waɗanda suke waje, da kuma waɗanda suke kai hari, ƙasa ta girgiza. Allah ne ya kawo wannan rikicewa.
16 Masu gadin Shawulu a Gebiya da take a Benyamin suka duba sai ga rundunar Filistiyawa a warwatsewa ko’ina. 17 Sai Shawulu ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ku ƙidaya mayaƙa ku ga wane ne ba ya nan.” Da suka ƙirga sai suka tarar Yonatan da mai ɗaukan makamansa ba sa nan.
18 Shawulu ya ce wa Ahiya, “Kawo akwatin alkawarin Allah.” (A lokacin akwatin alkawarin yana tare da Isra’ilawa.) 19 Yayinda Shawulu yake magana da firist kuwa, harguwa ya yi ta ƙaruwa a sansanin Filistiyawa. Sai Shawulu ya ce wa firist, “Janye hannunka.”
20 Sa’an nan Shawulu da dukan mutanensa suka taru suka tafi yaƙi. Suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna yaƙi da juna da takubansu. 21 Ibraniyawan da suke tare da Filistiyawa a dā, waɗanda suka bi Filistiyawan zuwa sansanin yaƙinsu, suka juya, suka goyi bayan Shawulu da Yonatan sa’ad da yaƙin ya taso. 22 Sa’ad da dukan Isra’ilawan da suka ɓuya a duwatsu a ƙasar Efraim suka ji labari cewa Filistiyawa suna gudu, sai suka fito suka fafare su. 23 Haka
24 A wannan rana, Isra’ilawa suka sha wahala ƙwarai domin Shawulu ya sa mutane suka yi rantsuwa cewa, “La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana, kafin in ɗauki fansa a kan abokan gābana.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.
25 Dukan rundunar ta shiga kurmi, sai ga zuma a ƙasa. 26 Da suka shiga ciki kurmin, suka ga zuma tana zubowa, duk da haka ba wanda ya sa yatsansa ya lasa saboda tsoron rantsuwar da suka yi. 27 Yonatan bai san cewa mahaifinsa ya sa mutane suka yi rantsuwa ba. Sai ya sa gindin sandan da yake hannunsa a saƙar zuma, ya kai bakinsa. Nan da nan sai ya ji ƙarfin jiki ya zo masa. 28 Sai wani soja ya gaya masa cewa, “Mahaifinka ya sa kowa ya yi rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana!’ Shi ya sa duk sojojin ba su da ƙarfi.”
29 Yonatan ya ce, “Mahaifina ya jefa ƙasar cikin matsala. Duba yadda na ji ƙarfin jiki sa’ad da na ɗanɗana wannan ’yar zuma mana. 30 Da yaya zai kasance ke nan da a ce an bar sojoji suka ci abincin da suka ƙwace daga abokan gābansu? Ai, da gawawwakin Filistiyawan da aka kashe sun fi haka.”
31 A ranan nan Isra’ilawa suka yi ta kashe Filistiyawa daga Mikmash har zuwa Aiyalon. Bayan haka gajiya ta kama su sosai saboda yunwa. 32 Sai suka yi warwason ganima, suka kwashe tumaki, da shanu, da maruƙa, suka yayyanka su, suka ci naman ɗanye. 33 Sai wani mutum ya ce wa Shawulu, “Duba, ga mutane suna zunubi ga
36 Shawulu ya ce, “Mu bi gangara mu fafare Filistiyawa da dare mu washe su har gari yă waye, mu kuma karkashe kowannensu, kada mu bar wani da rai.”
37 Saboda haka Shawulu ya tambayi Allah ya ce, “Mu bi bayan Filistiyawa? Za ka bashe su a hannun Isra’ila?” Amma Allah bai ba shi amsa a ranar ba.
38 Saboda haka Shawulu ya ce, “Ku zo nan dukanku shugabannin rundunoni, mu bincika mu san zunubin da ya kawo rashin amsan nan yau. 39 Muddin
40 Sai Shawulu ya ce wa dukan Isra’ilawa, “Ku tsaya a can, ni kuma da Yonatan ɗana mu tsaya a nan.”
41 Sa’an nan Shawulu ya yi addu’a ga
43 Sai Shawulu ya ce wa Yonatan, “Gaya mini mene ne ka yi.”
44 Shawulu ya ce, “Bari hukunci mai tsanani na Allah yă kasance a kaina, in ba ka mutu ba, Yonatan.”
45 Amma mutane suka ce wa Shawulu, “A ce Yonatan yă mutu bayan shi ya kawo babban nasara a Isra’ila? Faufau, muddin
46 Sai Shawulu ya daina bin Filistiyawa, suka koma ƙasarsu.
47 Bayan Shawulu ya hau karagar mulkin Isra’ila, ya yi yaƙi da abokan gābansu ta kowane gefe. Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, sarakunan Zoba, da kuma Filistiyawa. Duk wurin da ya juya, ya hore su. 48 Ya yi jaruntaka sosai, ya ci Amalekawa da yaƙi, ya kuma ceci Isra’ila daga hannuwan waɗanda suka ƙwace musu kaya.
49 ’Ya’yan Shawulu maza su ne, Yonatan, Ishbi, da Malki-Shuwa. Sunan babban ’yarsa ita ce Merab, ƙaramar kuma Mikal. 50 Sunan matarsa kuwa Ahinowam, ’yar Ahimawaz. Sunan shugaban ƙungiyar sojan Shawulu kuwa Abner ne ɗan Ner, shi Ner kuwa ɗan’uwan mahaifin Shawulu ne. 51 Mahaifin Shawulu, Kish da kuma Ner mahaifin Abner, ’ya’yan Abiyel ne.
52 Dukan kwanakin Shawulu sun kasance na yaƙe-yaƙe da Filistiyawa ne. Duk lokacin da Shawulu ya ga ƙaƙƙarfan mutum ko jarumi, sai yă ɗauke shi aikin sojansa.
<- 1 Sama’ila 131 Sama’ila 15 ->