1 Aka yi shekaru uku ba a yi yaƙi tsakanin Aram da Isra’ila ba. 2 Amma a shekara ta uku, Yehoshafat sarkin Yahuda ya gangara don yă ga sarki Isra’ila. 3 Sarkin Isra’ila ya ce wa shugabanninsa, “Ba ku san cewa Ramot Gileyad namu ne ba, duk da haka ba mu yi kome ba don mu sāke karɓanta daga sarkin Aram?”
4 Saboda haka ya tambayi Yehoshafat, ya ce, “Za ka tafi tare da ni don in yi yaƙi da Ramot Gileyad?”
6 Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa, kamar ɗari huɗu, ya tambaye su, “In kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada in kai?”
7 Amma Yehoshafat ya yi tambaya, ya ce, “Babu wani annabin
8 Sarkin Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, ya ce, “Akwai mutum guda har yanzu wanda ta wurinsa za mu iya nemi nufin
9 Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin shugabanninsa ya ce, “Kawo Mikahiya ɗan Imla nan take.”
10 Saye da rigunansu na sarauta, sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zama a kujerun sarautarsu a masussuka ta mashigin ƙofar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu. 11 Zedekiya ɗan Kena’ana kuwa ya yi ƙahonin ƙarfe ya kuma furta, “Ga abin da
12 Dukan sauran annabawan suka yi annabci iri abu ɗaya. Suka ce, “Ka yaƙi Ramot Gileyad, ka kuma yi nasara, gama
13 Ɗan aikan da ya je yă kawo Mikahiya, ya ce masa, “Duba, sauran annabawa suna maganar nasara wa sarki, sai ka ce mutum guda. Bari maganarka tă yarda da tasu, ka kuma yi maganar alheri.”
14 Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da
15 Da suka kai, sai sarki ya tambaye shi, ya ce, “Mikahiya, mu kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada mu kai?”
16 Sai sarki ya ce masa, “Sau nawa ne zan sa ka rantse cewa ba za ka faɗa mini kome ba sai dai gaskiya a cikin sunan
17 Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, kuma
18 Sai sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka cewa bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni, sai mummuna kawai ba?”
19 Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka ka ji maganar
22
23 “Saboda haka yanzu
24 Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya hau ya mari Mikahiya a fuska. Ya yi tambaya, “A wace hanya ce ruhu daga
25 Mikahiya ya amsa, “Za ka gane a ranar da ka je ka ɓuya a ciki cikin ɗaki.”
26 Sa’an nan sarkin Isra’ila ya umarta, “Ku kama Mikahiya, ku kai shi wurin Amon, shugaban birnin, da wurin Yowash ɗan sarki. 27 Ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku sa wannan mutum a kurkuku, kuma kada ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa, sai na dawo lafiya.’ ”
28 Mikahiya ya furta, “Idan har ka dawo lafiya, to,
29 Sai sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad. 30 Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama in shiga wurin yaƙi, amma ka sa kayan sarautarka.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya ɓad da kama, ya shiga cikin yaƙi.
31 Sarkin Aram kuwa ya umarci shugabanni kekunan yaƙinsa talatin da biyu, ya ce, “Kada ku yaƙe kowa, ƙarami ko babba, sai dai sarkin Isra’ila.” 32 Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙin suka ga Yehoshafat, suka yi tsammani, suka ce, “Tabbatacce wannan shi ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juye don su yaƙe shi, amma sa’ad da Yehoshafat ya yi ihu, 33 sai shugabannin kekunan yaƙin suka ga ashe ba sarkin Isra’ila ba ne, sai suka daina binsa.
34 Amma wani ya ja bakansa kawai ya bugi Ahab sarkin Isra’ila a tsakanin sassan kayan yaƙinsa. Sai sarki ya ce wa mahayin keken yaƙinsa, “Juye, ka fitar da ni daga yaƙin. An ji mini rauni.” 35 Dukan yini aka yi ta yaƙi, aka kuma riƙe sarki a keken yaƙinsa yana fuskanci Arameyawa. Jini daga mikinsa ya yi ta zuba a ƙasan keken yaƙin, a wannan yamma kuwa ya mutu. 36 Da rana tana fāɗuwa, sai kuka ta bazu cikin mayaƙa, “Kowane mutum ya tafi garinsu; kowa ya tafi ƙasarsa!”
37 Sai sarki ya mutu, aka kuwa kawo shi Samariya, aka binne shi a can. 38 Suka wanke keken yaƙi a tafki, a Samariya (inda karuwai suke wanka), sai karnuka suka lashe jininsa, kamar yadda maganar
39 Game da sauran ayyukan mulkin Ahab, haɗe da dukan abin da ya yi, da fadan da ya gina ya kuma shimfiɗa da hauren giwa, da biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. 40 Ahab ya huta da kakanninsa. Ahaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
41 Yehoshafat ɗan Asa ya zama sarkin Yahuda a shekara ta huɗu ta Ahab sarkin Isra’ila. 42 Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa, Azuba ’yar Shilhi. 43 A cikin kome ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa, bai kuma kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban
45 Game da sauran ayyukan mulkin Yehoshafat da abubuwan da ya yi, da kuma yaƙe-yaƙensa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 46 Ya kawar da karuwai maza na masujadai da suke kan tuddai waɗanda suka rage tun mulkin mahaifinsa Asa. 47 Babu sarki a lokacin Edom, saboda haka sai mataimaki ya yi mulki.
48 To, Yehoshafat ya gina jerin jiragen ruwan kasuwanci[a] don su je Ofir saboda zinariya, amma ba su yi tafiya ba, gama sun farfashe a Eziyon Geber. 49 A lokacin Ahaziya ɗan Ahab ya ce wa Yehoshafat, “Bari mutanena su tafi tare da mutanenka,” amma Yehoshafat ya ƙi.
50 Yehoshafat kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin Dawuda kakansa. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi.
51 Ahaziya ɗan Ahab ya zama sarkin Isra’ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta Yehoshafat sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekaru biyu. 52 Ya aikata mugunta a gaban
-
a Da Ibraniyanci na jiragen Tarshish