1 A lokacin Abiya, ɗan Yerobowam ya kamu da ciwo, 2 sai Yerobowam ya ce wa matarsa, “Ki tafi, ki ɓad da kama, don kada a gane ke a matsayin matar Yerobowam. Ki je Shilo. Annabi Ahiya yana a can, wannan wanda ya ce mini zan zama sarki a bisa wannan mutane. 3 Ki ɗauki dunƙulen burodi goma tare da ke, da waina, da tulun zuma, ki tafi wurinsa. Zai faɗa miki abin da zai faru da yaron.” 4 Saboda haka matar Yerobowam ta yi abin da ya faɗa, ta kuma tafi gidan Ahiya a Shilo.
6 Saboda haka sa’ad da Ahiya ya ji motsin sawunta a ƙofa, sai ya ce, “Ki shigo, matar Yerobowam. Me ya sa kike yi kamar wata ce dabam? An aiko ni wurinki da labari marar daɗi. 7 Je ki faɗa wa Yerobowam cewa ga abin da
10 “ ‘Saboda wannan, zan kawo masifa a gidan Yerobowam. Zan yanke kowane ɗa na ƙarshe a Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan ƙone gidan Yerobowam kamar yadda mutum yakan ƙone juji, sai duk ya ƙone ƙurmus. 11 Karnuka za su ci waɗanda suka mutu na Yerobowam a cikin birni, kuma tsuntsayen sararin sama za su cinye waɗanda suka mutu a jeji. Ni
12 “Ke kuma, ki koma gida. Sa’ad da kika taka ƙafa a birninki, yaron zai mutu. 13 Dukan Isra’ila kuwa za su yi makoki dominsa. Shi ne kaɗai na Yerobowam wanda za a binne, domin shi ne kaɗai a gidan Yerobowam wanda
14 “
17 Sai matar Yerobowam ta tashi ta tafi, ta kuwa tafi Tirza. Nan da nan da ta taka madogarar ƙofar gidan, sai yaron ya mutu. 18 Suka binne shi, dukan Isra’ila kuwa suka yi makoki dominsa, yadda
19 Sauran ayyukan sarautar Yerobowam, da yaƙe-yaƙensa, da yadda ya yi mulki, ba a rubuce suke a littafin tarihi na sarakunan Isra’ila ba? 20 Ya yi mulki shekaru ashirin da biyu, sai ya huta tare da kakanninsa. Sai Nadab ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
21 Rehobowam ɗan Solomon ya zama sarki a Yahuda. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekaru goma sha bakwai a Urushalima, birnin da
22 Yahuda ya aikata mugunta a gaban
25 A shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam, Shishak sarkin Masar ya kai wa Urushalima yaƙi. 26 Ya kwashe dukiyar haikalin
29 Game da sauran ayyukan mulkin Rehobowam kuwa, da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 30 Aka ci gaba da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam. 31 Sai Rehobowam ya huta da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita kuwa mutuniyar Ammon ce. Sai Abiyam[a] ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
<- 1 Sarakuna 131 Sarakuna 15 ->-
a Waɗansu rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci da Seftuwajin (duba kuma 2Tar 12.16); yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci suna da Abiya